(ABNA24.com) Shugaban kasar Afganistan, Ashraf Ghani, da abokin hamayyarsa Abdullah Abdullah, sun cimma yarjejeniyar yin aiki tare.
Yarjejeniyar da bangarorin suka cimma a yau ta tanadi Abdullah Abdullah, ya jagoranci kwamitin hadin kan ‘yan kasar, wanda kuma ake fatan zai kawo karshen rikicin siyasar kasar.
Da yake sanar da hakan kakain shugaban kasar ta Afganistan, Sediq Sediqqi, ya ce an cimma matsaya ta yadda bangarorin zasu raba iko tsakaninsu, za’a kuma nada wasu mambobin Abdullah Abdullah a cikin kwamitin na hadin kan kasa.
A cen baya dai mutanen biyu ko wanne ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 9 ga watan Maris da ya gabata.
/129
18 Mayu 2020 - 04:31
Lambar labari: 1037785
Shugaban kasar Afganistan, Ashraf Ghani, da abokin hamayyarsa Abdullah Abdullah, sun cimma yarjejeniyar yin aiki tare.